Kotu taki sakin matar da ta kashe mijinta
Wata Kotu a Faransa tayi watsi da bukatar sakin Jacqueline Sauvage mai shekaru 68 data kashe mijinta a shekarar 2012 kan galaza mata da ya keyi.
Wallafawa ranar:
Watsi da bukatar na zuwa ne duk da cewa gwamnatin faransa ta bukaci ayi mata afuwa bayan jama’a kimanin 400,000 sun sanya hannu bisa wata takarda da suka gabatar na bukatar sakin Jacqueline Sauvage.
Sai dai ofishin masu gabatar da kara a kasar ya ce za’a daukaka kara don ganin Sauvage ta samu afuwa.
A watan Fabairun daya gabata aka sauyawa Sauvage mazauni zuwa gidan yarin Reau dake kudancin Paris domin duba lafiyar kwakwalwar ta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu