Belgium
Wani mutun ya kai harin adda a Belgium
Wani mutun dauke da adda ya raunata jami’an ‘yan sanda mata guda biyu a birnin Charleroi da ke kudancin Belgium.
Wallafawa ranar:
Talla
Rahotanni sun ce, an ji maharin na yin kabbara a lokacin kaddamar da farmakin na yau, kafin daga bisani 'yan sanda su harbe shi har lahira.
Firaministan kasar, Charles Michael ya katse hutunsa da ya ke yi a kudancin Faransa, inda zai koma Belgium don halartar taron tattauna batun tsaron kasar a gobe Lahadi.
Tun lokacin da kungiyar IS ta kashe mutane 32 a birnin Brussels a cikin watan Maris, kasar ta Belgium ta tsaurara matakan tsaro .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu