Isa ga babban shafi
Italiya

'Yan Sandan Italiya su karbe kadarorin 'Yan Mafiya

‘Yan sandan kasar Italiya sun yi nasarar karbe kadarorin wasu gungun ‘yan mafiya da darajarsu ta haura sama da dala miliyan dubu biyu bayan jerin samamen da suka kai a kan ‘yan mafiyan da suka addabi kasar. 

'Yan Sandan Italiya cafke da daya daga cikin 'Yan Mafiyan
'Yan Sandan Italiya cafke da daya daga cikin 'Yan Mafiyan
Talla

An dai kai samamen ne kan ‘Yan mafiyan da ake wa lakabi da Ndrangheta da ayyukan su ya kun shi safarar hodar Iblis zuwa yankin nahiyar Turai .

Hakazalika an kwace kamfanoni sama da 60 da gidajen caca masu tarin yawa tare da wasu kadaddarori na daban.

Shugaban ‘yan mafiyan mai suna Mario Gennaro ya shahara saboda irin nasararorin da ya samu a caca da safarar hodar Iblis a sassa dabam dabam.

kungiyar ta kuma shahara ganin yadda ta zarta sauran kungiyoyi ire iren su dake gudanar da ayyukansu a yankin sakamakon dimbin dukiyar da ta tara ta hanyar safarar hodar iblis zuwa kasashen latin Amurka da nahiyar Turai zuwa arewacin Africa dama kudancin kasar ta Italiya.

Yanzu haka dai hukumomin kasar sun bazama neman wasu mutane 28 da ake zargi da kafa gidajen caca yayin da wasu 23 ke tsare karkashin sa idon hukumomin.

makwanni biyu da suka gabata hukumomin kasar ta Italiya sun karbe kadarori da darajarsu ta zarta Euro biliyan daya daga kungiyar mafiya na iyalan Sicily tare da kamfanoni 33 da daruruwan gidaje tare da motoci sama da 40 .
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.