Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane sun mutu sakamakon fashewar bututun Man fetir a Najeriya

A tarayyar Najeriya, fashewar wani bututun man fetur na katafaran kamfanin hakar man fetir na kasar Italiya Eni ta yi sanadiyar mutuwar mutane 12 a yayinda wasu guda uku suka samu munanan raunuka, kamar yadda kamfanin man na Eni ya sanar a yau juma’a.

Wani kamfanin hada hadar Man Fetir
Wani kamfanin hada hadar Man Fetir AFP PHOTO / MAHMUD TURKIA
Talla

An dai bayyana cewa hatsarin ya faru ne a daidai lokacin da kamfanin ke gyaran bututun da yan tsagera suka fasa a yankin Niger Delta dake kudancin kasar ta Nigeria mai arzikin man fetur.

A bangare guda, kamfanin y ace, akwai dan sarkakiya dangane da aukuwar lamarin dake bukatar warware wa yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike game da hatsarin.

Kamfanin na Eni na daya daga cikin manyan Kamfanonin Mai na kasashen ketare dake aiki a Najeriya kuma Najeriya ce ta fi arzikin man fetir a Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.