An kai harin Bom a ofishin jakadancin Italiya dake Masar
Yau Asabar mutum 1 ya rasa ransa, sakamakon wani Bom da ya fashe a ofishin jakadancin kasar Italiya dake birnin Alkahiran kasar Masar. Wakilin kamfanin dillancin labarun Faransa na AFP ya bayyana cewa fashewar, an dasa Bom a cikin wata mota da aka ajiye a kusa da ofishin, kuma lamarin yayi sanadiyyar lalacewa wani sashe na ofishin jakadancin.
Wallafawa ranar:
Jami’an kula da lafiya a wajen, sun ce fashewar da ta faru da misalin karfe 6 da rabi na safe agogon kasar ta Masar, tayi sanadiyar raunata wasu ‘yan sanda 2 dake kula da wurin.
Tuni hukumomin birnin Rome suka yi Allah wadai da harin, sai dai sun ce harin bai shafi dan kasar ta Italiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu