Isa ga babban shafi
Jamus-Masar

Jamus ta kalubalanci kasar Masar kan hukuncin kisa

Jamus ta kalubalanci kasar Masar akan yin amfani da hukunci kisa akan masu laifi, sai dai kuma ta lashin takobin baiwa kasar haddin kai wajen yaki da masu tsaurara ra’ayin addini. Wannan dai na zuwa ne yayin wata ziyarar kwanaki 2, da shugaban Masar Abdelfatah Al-sisi ya kai kasar ta Jamus, da nufin inganta huldar kasuwanci, sai dai kuma ziyarar ta haifar da zanga-zanga a jamus din.Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta jadada rawar da kasar Masar zata iya takawa wajen samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, dama yankuna Afrika da ke fama da ayukan ta’adanci.A wani taron manema labari da aka gudanar da birinin Berlin, Merkel ta ce tana gani baiwa Masar haddin kai a huldar kasuwanci, zai taimaka matuka wajen samar da daidaito a yankin Arewacin Afrika.Sai dai kuma ta kalubalanci batun hukunci kisa da kotunan kasar ta Masar ke yankewa, inda tace bai dace ba.Karewar zantarwa shugababnnin 2 ke da wuya, sai zanga-zanga ta barke a dakin taron da kuma titunan kasar Jamus, kan tarba da aka yiwa al-Sisi a Jamus.A ranar litinin data gabata ne kungiyoyin kare hakkin dan’adam suka bukaci Angela Merkel data matsawa al-Sisi ya kawo karshen rikice-rikicen kasar, da aka shafe tsahon lokaci yaki ci, yaki cinyewa da kuma batun matsawa kungiyoyin adawan kasar.Sai dai kuma a nashi bangaran, Abdelfatah al-Sisi na gani cewa kotun kasar masar na yankewa mutane hukunci ne dai-dai da abin da laifin da suka aikata. 

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel 路透社
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.