Isa ga babban shafi
Syria-Jamus

Jamus zata kara yawan 'yan gudun hijira da take karba daga Syria

Kasar Jamus ta bayyana shirinta na kara karban ‘yan gudun hijirar kasar Siriya 10,000, sai dai Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kara kira ga kasra ta Jamus da ta kara yawan ‘yan gudun hijirar da za ta iya dauka daga Siriyar mai fama da yaki tsakanin ‘yan tawaye da Gwamnati.Kasar Jamus dai na kafa hujja ne da shirinta na taimakawa al’umma, don haka Ministan harkokin cikin Gidan kasar Thomas de Maiziere ya ce suna da niyyar kara yawan ‘yan gudun hijira da zasu karba.Ministan yace gwamnatin taraiyya, da na larduna kasar duk sun amince su ninka yawan ‘yan gudun hijiran da suke zuwa daga Syria.Kafin wannan sanarwar, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty ta bayyana matakin da Jamus ke dauka a matsayin wanda bai taka kara ya karya ba, inda kungiyar tace har yanzu akwai ‘yan gudun hijiran da ke shiga hatsari kafin su iso Jamus.Yakin na Syria, da aka shafe fiye da shekaru 3 ana gwabzawa, ya lakume rayukan fiye da mutane dubu 162, yayin da fiye da rabin ‘yan kasar suka tsere daga gidajensu. 

Shugaban Syria, Bashar al-Assad
Shugaban Syria, Bashar al-Assad Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.