Isa ga babban shafi
Syria-MDD

Kasashen duniya sun nemi a kawo karshen rikicin kasar Syria

Wakilan manyan kasashen duniya da ke halartar taron sasanta bangarorin da ke hamayya da juna a kasar Syria, wanda aka buda yau laraba a birnin Montreux na kasar Swilzerland, sun bukaci gwamnati da kuma ‘yan adawar kasar da su kawo karshen yakin basasar kasar. Akwai dai wakilan manyan kasashen duniya da na gwamnatin Syria da kuma ‘yan adawar kasar a wannan taro da ke gudana a karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya.Babban magakatarda na MDD Ban Ki-moon ne ya jagoranci bikin bude taron, da kasashen duniya masu ruwa da tsaki a wannan batu suka jima suna kokarin ganin an gudanar da shi domin warware rikicin da aka shafe watanni 35 ana fama da shi a kasar.Yayin da magatakardan ke bayyana taron a matsayin wata babbar dama domin cimma masalaha a tsakanin mahalartansa, ministan harkokin wajen kasar ta Syria Walidul Mu’allem kuwa cewa ya yi Assad ba ya da niyyar sauka daga mukaminsa.Jagoran kawance adawar kasar ta Syria Ahmad Jarba, ya bukaci Bashar Assad da ya gaggauta amincewa da kafa sabuwar gwmnatin rikon kwarya a kasar.Shi kuwa Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya jaddada cewa Assad ba zai kasance a cikin sabuwar gwamnatin da ake shirin kafawa a kasar ba, takwaranshi na kasar Rasha Sergei Lavrov, cewa ya yi taron ba abu ne mai sauki ba sannan kuma ba gaggawa a cikinsa.A jimilce dai kasashe 40 ne ke halartar zaman na birnin Montreux da za a share kwanaki 7 zuwa 10 ana gudanar da shi. 

Mahalarta taron zaman lafiyar Syria da ake yi a Montreux
Mahalarta taron zaman lafiyar Syria da ake yi a Montreux REUTERS/Jamal Saidi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.