Isa ga babban shafi
Syria-Amurka

Amurka ta nemi 'yan tawayen Syria su halarci taro Geneva

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya sake yin kira ga ‘yan adawar kasar Syira da su jingine bambance-bambancen da ke tsakaninsu domin halartar taron birnin Geneva a cikin makon gobe, wanda a lokacinsa ake fatar samar da mafita ga rikicin da kasar ta Syria ke fama da shi. Kerry, wanda ke zantawa da manema labarai a cikin daren jiya, ya ce taron na birnin Geneva, wata babbar dama ce ga ‘yan adawar domin cimma muradun da suka sa al’ummar Syria suka kaddamar da boren juyin juya hali a kasarsu.A can kuwa birnin Moscow na kasar Rasha, tawagar manyan jami’an gwamantin Syria da kuma na kasar Iran na can na gudanar da nasu taro domin shiryawa wannan taro na binrin Geneva. 

REUTERS/Pablo Martinez Monsivais/Pool
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.