Isa ga babban shafi
Syria-MDD

Italiya ta bayar da wajen da za a lalata makaman kasar Syria

Kasar Italiya ta bayyana tashar jirgin ruwan da za a yi amfani da ita, wajen lalata sunadaran makai masu guban da aka fara kwashewa daga kasar Syria. Tuni ‘yan kasar ta Italiya suka fara Allah wadai da wannan mataki, yayin da hukumar sa ido kan makamai masu guba kuma ke kokakarin hanzarta safarar sunadaran.Ministan Sufurin kasar ta Italiya Maurizio Lupi yace hukumomin kasar sun zabi tashar jirgin ruwan Gioia Tauro, a matsayin inda ya dace a yi wannan gagarumin aikin.Lupi yace sun kiyasta cewa za a sauke sundukai kimanin 60, da ke kunshe da sunadaran, kuma ba za a ajiye su a doron kasa ba.Shugaban hukumar yaki da yaduwar makamai masu guba ta OPCW, da ke gudanar da aikin, Ahmet Uzumcu, ya yi godiya ga hukumomin na birnin Rome, da suka bayar da tashar ruwan, da za a gudanar da aikin.Uzumcu yace a farkon watan Fabarairu mai zuwa, za a fara aikin, da zai gudana cikin sa’oi 48.Sai dai magajin garin Gioia Tauro, da ke kudanci Italiya, Renato Bellofiore ya caccaki shirin da ya ce mai cike da kasada, ida yace a shirye suke su dauki mataka shari’a don hana aikin.Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kudurin lalata makaman na Syria, bayan daruruwan mutane sun mutu sakamakon harin da akai kai da makamai masu guba a shekarar bara, da gwamnati da ‘yan tawayen kasar ke nuna wa juna dan yatsa akai. 

Dan rajin kare hakkin dan Adam a Syria, sanye da hular kariya daga makamai masu guba
Dan rajin kare hakkin dan Adam a Syria, sanye da hular kariya daga makamai masu guba REUTERS/Bassam Khabieh
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.