Birtaniya na cikin kasashen da ke yaki da ISIL
Birtaniya ta shiga sahun kasashen Amurka da Canada da ke yi wa Mayakan IS ruwan wuta da jiragen sama a Syria kamar yadda wata majiyar tsaro ta tabbatar, duk da majalisar kasar ta ki amincewa da matakin a shekarar 2013.
Wallafawa ranar:
Kakakin Firaministan kasar David Cameron ya ce jiragen kasar marar sa matuka na cikin jerin jiragen Amurka da ke yi wa mayakan IS luguden wuta.
Amma ma’aikatar tsaron kasar ta musanta zargin, tana mai cewa babu wani matuki jirgin Birtaniya a Syria.
Yanzu haka kuma wasu ‘Yan Majalisar kasar sun bukaci Ministan tsaron Birtaniya ya yi mu su bayani akan matakin bayan sun yi watsi da bukatar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu