Isa ga babban shafi
Afghanistan

An kashe wani kwamanda ISIL a Afghanistan

Dakarun sojoji sun tabbatar da kashe kwamanda kungiyar ISIL da ke jagoranta hare-hare a yankuna Afghanistan da pakistan a wani harin kurman  jirgin sama da aka kai gabashin Afganistan.

DR
Talla

A cewar rundunar tsaron kasar an kashe Hafiz Saeed tare da mukarabansa 30 a harin sama da dakarunsu suka kaddamar a jiya Juma’a a lardin Nangarhar kusa da iyakar Pakistan.

Lamarin da ke zuwa bayan hukumomin Afganistan sun tabbatar da mutuwar akalla yara uku, a wani tashin bam da ya auku a garin Kandahar da ke kudancin kasar

‘Yara da basu haura shekaru 10 ba, na zaune ne a cikin wani shago inda suka nemi mafaka saboda tsanani zafi ranar, lokacin da bam din da aka boye a shagon ya fashe, tare da jikata wasu 6 daga cikinsu kamar dai yadda mai magana da yawun ‘yan sanda yankin Zia Durani ya sanar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.