Isa ga babban shafi
Afghanistan

Afghanistan za ta ci gaba da tattaunawa da Taliban

Kasar Afghanistan tace za ta ci gaba da tattaunawa da Taliban a kasar Pakistan, domin amincewa da matakan da suka dace wajen kawo karshen rikicin kasar na tsawon shekaru 40.

Mayakan Taliban sun shafe shekaru 13 suna yaki a Afghanistan
Mayakan Taliban sun shafe shekaru 13 suna yaki a Afghanistan
Talla

A ranar Talata ne aka soma zaman tattaunawa tsakanin bangaren ‘Yan Taliban da gwamnatin Afghanistan a Pakistan a wani kokari na ganin a kawo karshen rikicin kasar.

Bangarorin biyu sun kama hanyar cim ma nasara a zaman tattaunawar su ta farko da suka yi a kasar Pakistan duk da wasu hare hare da ‘yan kungiyar Taliban suka kai kafin soma zaman.

Zaman wanda aka kwashe tsawon awanni ana yin shi an wanye lafiya inda bangarorin biyu suka amince da ci gaba da tattaunawar bayan Azumin Ramadan.

Mai shiga tsakani Din Mohammad ya sanarwa manema labarai cewa makasudin wannan zama shi ne kawo karshen zub da jini.

A na shi bangaren mai wakiltar gwamnatin kasar Afghanistan ministan harkokin cikin gida Hekmata Khalil Karzai ya kasance wani babban jami’I a kasar da ya taba zama da ‘yan kungiyar Taliban

Karzai ya ce ba shi da tabbacin yadda al’amura za su kasance amma akwai alamun samun nasara a wannan zama ganin yadda a wannan karon wadanda suka wakilici bangaren Taliban ma su fada a ji ne a kungiyar.

Dubban mutane ne suka rasa rayukan su sakamakon hare haren yan kungiyar Taliban a cikin kasashen Pakistan da Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.