Isa ga babban shafi
Afghanistan

Taliban ta kashe Sojojin Afghanistan 11

Akalla Sojojin Afghanistan 11 kungiyar Taliban ta kashe a wani harin kwantan bauna da mayakanta suka kai Yammacin kasar, a dai dai lokacin da sojojin ke yaki da kungiyar ba tare da taimakon kungiyar NATO ba.

Jami'an tsaron Afghanistan a kusa da ginin Majalisa da aka kai hari a Kabul
Jami'an tsaron Afghanistan a kusa da ginin Majalisa da aka kai hari a Kabul REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

Mai Magana da yawun Gwamnan Yankin Heirat, Ehsanullah Hayat, ya ce mayakan sun kai harin kan sojin ne jiya da yamma lokacin da suke wucewa a cikin motar su.

Kakakin sojin Yankin Najibullah Najibi wanda ya tabbatar da harin yace akwai Sojoji hudu da suka samu rauni.

Tun a watan Disemba ne shirin NATO ya kawo karshe a Afghanistan bayan shafe shekaru 13 suna yaki da Taliban a kasar amma akwai wasu sauran Sojoji kasashen waje da ke bayar da horo ga Jami’an tsaron Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.