Isa ga babban shafi
Pakistan-Afghanistan

Mutane 150,000 suka mutu a rikicin Pakistan da Afghanistan

Wani rahoto da wata cibiya mai zaman kanta a kasar Amurka ta gudanar na cewa yaki da aka yi a kasar Pakistan da Afghanistan daga shekara ta 2001 zuwa yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji da fararen hula dubu 150.

Sojojin Afghanistan na harba makaman Atilare akan Mayakan Taliban a yankin Kunduz
Sojojin Afghanistan na harba makaman Atilare akan Mayakan Taliban a yankin Kunduz Reuters/路透社
Talla

Binciken da Cibiyar Watson mai mazauninta a sashen nazarin harkokin duniya a Jami’ar Brown da ke Amurka suka gudanar na cewa akwai Karin mutane dubu 162 da aka jikkata tun lokacin da sojojin kawance bisa jagorancin Amurka suka fara kai wa Mayakan Taliban hare-hare bayan harin 11 ga watan Satumba da aka kai wa Amurka.

Masu binciken na cewa rikicin kasar Afghanistan sai kara ruruwa ya ke yi a kullum.

Masanan na cewa a kasar Pakistan rikicin ya ragu ba kamar da fari ba.

Masanan sun mayar da hankula ne game da rasa rayukan da aka samu sakamakon harsasai da manyan bindigogi da bama-bamai da aka yi amfani da su a fagen yaki.

Mawallafin sakamakon binciken Neta Crawford na cewa nazarin da suka fara tun fara yake-yaken, na nuna munin yaki, kasancewar hasarar duk rai daya akwai wasu mutane akalla 15 dake rabe da mamacin wadanda suma tamkar kashe su aka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.