Isa ga babban shafi
Pakistan

An cafke Mayakan Taliban 12 da suka kai hari a Peshawar

Rundunar sojin kasar Paskitan ta bayyana cafke wasu Mayakan Pakistan 12 da ake zargi sun kai wa daliban Makaranta munmunan hari a Peshawar inda aka kashe mutane 150. Sojojin Pakistan sun ce suna ci gaba da farautar wasu mayakan guda shida bayan cafke mutane 12 da suka kai hari a wata makaranta a Peshawar inda suka kashe mutane 150 a watan Disemba.

Harabar Makarantar da Taliban ta kai hari a Peshawar
Harabar Makarantar da Taliban ta kai hari a Peshawar REUTERS/Khuram Parvez
Talla

Kakakin rundunar Sojin Pakistan Janar Asim Bajwa ya shaidawa manema labarai cewa gungun mayaka 27 ne suka kai hari, yayin da aka kashe 9 daga cikinsu tare da cafke 12.

Sojojin na Pakistan sun ce mayakan na Taliban na buya ne a Afghanistan, kuma a cewar Janar Bajwa, shugaban Taliban Mullah Fazlullah ne ya bayar da umurnin a kai harin kamar yadda daya daga ikin wadanda aka cafke ya tabbatar wa Sojojin.

Sojojin Pakistan sun ce suna aiki tare da mahukuntan Afghanistan domin cafko shugaban Taliban.

Dukkanin mutanen 12 da aka cafke suna hannun mahukuntan Pakistan yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.