Isa ga babban shafi
Pakistan

An hukunta ‘yan Taliban din da suka harbi Malala

Kotu a kasar Pakistan ta yanke wa mutane 10 hukuncin daurin rai da rai a gidan yari bayan kama su da laifin yunkurin kashe Malala Yousafzai daliban nan mai fafutikar tabbatar da ilimin ‘yaya mata a shekarar 2012.

Malala Yousafzai
Malala Yousafzai REUTERS/Darren Staples
Talla

A cikin watan oktobar shekarar 2012 ne dai, mayakan Taliban suka harbi Malala Yousafzai a kai a lokacin da take cikin wata motar ‘yan makaranta.

Wannan al’amari da ya raunana Malala da wasu dalibai guda biyu ya ja hankalin duniya musamman kasashen yammaci, da suka yi jinyar malala a Birtaniya.

Yanzu haka kuma kotun Pakistan ta daure mutane 10 daurin rai rai.

Kuma tsarin dokar Pakistan shekaru 25 ne hukuncin daurin rai da rai, amma kuma mutanen na da ‘yan daukaka kara.

Tun a watan Satumban 2014 ne rundunar tsaron Pakistan tace ta cafke mutanen 10 da zargin.

Sai dai cikin mutanen babu wanda ake zargi ya harbi Malala Ataulla Khan wanda ake hasashen yana buya a Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.