Isa ga babban shafi
Najeriya

Chibok: Malala ta kawo ziyara a Najeriya

Malala Yousafzai, Dalibar kasar Pakistan da Mayakan Taliban suka harba akan gwagwarmayar da take yi na ilimin ‘yaya mata ta kawo ziyara a Najeriya, inda ta gana da wasu iyayyen ‘Yan matan da mayakan Boko haram suka sace sama da 200 a garin Chibok.

Malala Yousafzai da ke gwagwarmayar tabbatar da ilimin 'yaya mata a Pakistan
Malala Yousafzai da ke gwagwarmayar tabbatar da ilimin 'yaya mata a Pakistan REUTERS/Gary Cameron
Talla

A gobe litinin ne ake sa ran Malala, zata gana da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, a dai dai lokacin da aka shafe watanni uku da sace ‘Yan mata kimanin 276 a garin Chibok a cikin Jahar Borno.

Dalibar kuma ta gana da kungiyoyin da ke fafutikar ganin an sako ‘Yan matan a Najeriya tare da yin kira ga gwamnatin Najeriya ta hanzarta wajen ganin an kubutar da ‘Yan matan da aka sace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.