Pakistan-Syria
Malala ta nemi a ilmantar da ‘Yan gudun hijira a Syria
Matashiya mai fafutukar ganin an bai wa ‘ya’ya mata ilimi a kasar Pakistan, Malala Yousufzai, ta bukaci shugabannin kasashen duniya su bayar da gudumawar kudi Dala Miliyan 175 don ilmantar da dimbin yara ‘Yan gudun hijirar da suka kwararo zuwa kasashen da ke makwabtaka da kasar Syria.
Wallafawa ranar:
Talla
Malala tace tana jin zafin abinda ya ke faruwa a kasar Syria, domin sun taba fuskanci irin matsalar a kasar Pakistan.
Hukumar kula da ilimin yara ta Majalisar Dinkin Duniya tace yaran Syria 257,000 ke neman ilimi a Lebanon, inda tace adadin na iya akaruwa zuwa 400,000.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu