Afghanistan ta koma teburin sulhu da Taliban
Tawagar Gwamnatin kasar Afghanistan ta soma zaman tattaunawa da Mayakan Taliban a Pakistan da nufin samun jituwa don kawo karshen rikicin Mayakan na tsawon shekaru 13.
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar harakokin wajen Pakistan ta fadi a cikin wata sanarwa cewa Tawagar Afghanistan sun gana da wakilan Taliban a garin Murree da ke arewacin Islamabad.
Sanarwar tace bangarorin biyu sun tattauna matakan da ya kamata a dauka domin tabbatar da zaman lafiya a Afghanistan. Sanarwar kuma ta kara da cewa bangarorin biyu sun amince su sake tattaunawa idan an idar da Azumin watan Ramadan.
Mai Magana da yawun shugaban kasar Sayed Zafar Hashemi ya ce tawagar gwamnatin na karkashin mataimakin ministan harkokin wajen kasar ne Hekmat Khalil Karzai.
Kungiyar Taliban ba ta fito fili ta bayyana shirin shiga taron ba, amma daya daga cikin shugabanin ta ya ce sun tafi kasar Pakistan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu