Za a daure masu bayar da bayanan da ke saba wa na gwmanati
Gwmanatin Masar na shirin kafa sabuwar doka da ke bayar da damar daure duk wani dan jarida da ya wallafa alkalumman ‘’karya’’ game da dakarun kasar da suka mutu sakamakon harin ta’addanci.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wannan dai na kunshe ne a cikin wani sabon daftarin doka da gwamnatin kasar ke shirin kafawa domin kawo karshen yadda ake samun bambancin alkalumma tsakanin na hukumomi da kuma wadanda ‘yan jarida ke bayarwa a duk lokacin aka kai wa jami’an tsaron kasar hari.
Yanzu haka dai gwamnatin Abdel Fatah Al-sisi ya kuduri aniyar murkushe duk wadanda ke neman yi wa gwmnatinsa hawan kawara, da suka hada da ‘yan adawa da kuma ‘yan jaridu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu