Isa ga babban shafi
Masar

Shekaru biyu da hambarar da Morsi a Masar

An cika shekara biyu a yau Juma’a da Sojojin Masar suka hambarar da gwamnatin Mohammed Morsi na Jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi zababben shugaban kasa na farko a kasar.

Hambararren Shugaban Masar Mohamed Morsi
Hambararren Shugaban Masar Mohamed Morsi AFP PHOTO / STR
Talla

A ranar 3 ga watan Yuli ne Babban hafsan Sojin Masar wanda a yanzu shi ne shugaban kasa Abdel Fattah al Sisi ya hambarar da Morsi bayan shafe kwanaki ana zanga-zangar kin jinin gwamnatin ‘Yan uwa musulmi.

Tun lokacin ne kuma mahukunatan Masar karkashin jagorancin Morsi ke kamewa tare da kashe magoya bayan Morsi.

An kashe daruruwan mutane tare da kame dubbai da yanke wa daruruwa hukuncin kisa.
Morsi na cikin wadanda aka yanke wa hukuncin kisa tare da wasu manyan shugabannin Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi.

Yanzu haka kuma Masar na ci gaba da fuskantar hare hare daga Mayakan IS a yankin Sinai inda aka hallaka rayukan mutane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.