Isa ga babban shafi
SYRIA

Sojojin kawance sun kai hare-hare kan mayakan ISIS

Dakarun kawancen kasashen duniya karkashin jagorancin Amurka sun kai hare-hare ta sama a kan mayakan da ke da’awar jihadi a garin Raqa na kasar Syria, inda rahotanni ke cewa an kashe mayakan na ISIS akalla 30 tare da lalata sansanoninsu.

Harim Amurka kan mayakan ISIS
Harim Amurka kan mayakan ISIS Reuters
Talla

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun gwamnatin Bashar Assad da ke samun goyon bayan zaratan mayakan kungiyar Hizbollah suka samu nasarar kutsawa a cikin garin Zabadani na lardin Qalamun kusa da iyakar Syria da Lebanon, bayan sun fatattaki mayakan na ISIS daga garin.

A can kuwa yankin arewacin kasar ta Syria, dakarun Assad na can na fafatawa da ‘yan tawaye da kuma mayakan da ke da’awar jihadin, wadanda suka kulla sabon kawance da nufin tunkarar sojojin gwmanatin a yankin Alep.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.