Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy ya lashe zaben shugabancin UMP

An zabi tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy a matsayin shugaban Jam’iyyarsa ta UMP mai adawa, a wani mataki da zai ba shi damar dinke barakar Jam’iyyar domin lashe zaben shugaban kasa a 2017.

Nicolas Sarkozy, tsohon shugaban Faransa
Nicolas Sarkozy, tsohon shugaban Faransa EUTERS/Ian Langsdon/Pool
Talla

Nicolas Sarkozy ya samu rinjayen kuri’u sama da kashi 64 a zaben shugabancin Jam’iyyarsa da aka gudanar a karshen mako.

Kuma wannan dama ce ga Sarkozy ya dinke barakar Jam’iyyarsa domin tunkarar zaben shugaban kasa.

Jam’iyyar UMP da Charles de Gaulle ya samar bayan kammala yakin duniya na biyu tana fama da matsalolin cikin gida amma Sarkozy yace zai hada kan ‘ya’yan jam’iyyar, tare da shan alwashin lashe zaben shugaban kasa, kamar yadda ya sanar a shafin shi na Facebook.

Sai dai masu fashin bakin siyasa a Faransa suna ganin yawan kuri’un da Sarkozy ya samu kalubale ne gare shi musamman a kokarin jagorantar Jam’iyyar UMP ga nasarar kawo karshen mulkin Jam’iyyar gurguzu ta Francois Hollande.

Gwamnatin Hollande da ke fuskantar suka a Faransa, yanzu dama ce ga Sarkozy ya shata makomar Faransa mai kyau a yakin neman zaben Jam’iyyarsu kafin zaben 2017.

Amma babban kalubalen da ke gaban Sarkozy yanzu shi ne lashe zaben fitar da gwani da Jam’iyyar UMP zata gudanar a 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.