Isa ga babban shafi
Faransa

Ana son a ci zarafina-Sarkozy

Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy, ya yi zargin cewa an bukaci ya gurfana a gaban ‘yan sanda ne domin kawai ana da niyyar cin zarafinsa. Tsohon shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke zantawa da wata kafar yada labarai da ke kasar, bayan da jami’an tsaro suka tsare shi na tsawon sa’o’i 15 bisa zargin karbar rashawa.

Nicolas Sarkozy, tsohon shugaban Faransa
Nicolas Sarkozy, tsohon shugaban Faransa TF1
Talla

Sarkozy ya yi zargin cewa an gurfanar da shi a gaban ‘yan sanda ne domin kawai ana da niyyar tozartar da shi a idon duniya, yana mai cewa ba wani laifin da ya aikata da zai sa a gayyace shi tare da yi masa tambayoyi har tsawon lokaci bisa zargin rashawa.

Tsohon shugaban yace bai taba cin amana ba ko taka dokokin kasar Faransa ba, yana mai danganta lamarin da cewa siyasa ce ke neman yin shisshigi a cikin al’amurran shari’a domin dakushe kwarjinin da ya ke da shi a idon jama’a.

Sai dai shugaban kasar Francois Hollande, ya bayyanan cewa har yanzu Sarkozy yana a matsayin wanda bai aikata laifi ba har zuwa lokacin da kotu ta tabbatar da shi a matsayin mai laifi, tare da nisanta gwamnati akan tana da hannu wajen kaddamar da binciken da alkalai ke yi a kansa tsohon shugaban.

Ana dai tuhumar Nicolas Sarkozy ne da hannun wajen karbar rashawa musamman ma a lokacin yakin neman zabensa a shekara ta 2007, lamarin da ke iya shafar makomarsa a siyasance musamman ma idan aka yi la’akari da cewa akwai yiyuwar Sarkozy ya bukaci ya sake tsayawa takarar neman shugabancin kasar a zabe mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.