Isa ga babban shafi
Faransa

Kotun Faransa ta yi watsi da bukatar Sarkozy

Wata Kotu a Fraansa ta yi watsi da bukatar tsohon shugaban kasar, Nicolas Sarkozy na ganin an mayar masa da littafin da ya ke tara bayanai da jami’an tsaro suka karbe, lokacin da suke gudanar da bincike akan sa.

Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy
Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy REUTERS/Eric Gaillard
Talla

Sarkozy da ke tunanin yin takarar zabe nan gaba, na hangen cewar ana iya amfani da bayanan wajen tuhumarsa kan karbar cin hancin.

An dai yi watsi da zargin da ake masa a watan Octoba na bara, amma kuma an tura wasu jami’ansa guda 10 don fuskantar shari’ar karbar kudin yakin neman zabe daga attajira Lilian Betancourt.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.