Isa ga babban shafi
Faransa

‘Yan adawa sun nemi a dakile ba bakin haure shedar zama Faransawa

Jam’iyyar UMP ta tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy za ta gabatar da wani kudiri a Majalisa da zai dakile ba ‘yayan bakin haure da aka Haifa a cikin kasar shedar zama ‘yan kasa, wannan kudirin kuma ya janyo suka daga bangaren ‘yan kishin kasa.

Jean-François Copé, Sakataren Jam'iyyar UMP
Jean-François Copé, Sakataren Jam'iyyar UMP Photo d'archives/REUTERS/Benoît Tessier
Talla

Shugaban Jam’iyyar ta UMP Jean-Francois Cope yace zasu gabatar da kudirin ne a gaban Majalisa a farkon 2014 wanda aka tsara domin sake fasalta tsarin dokar shige da fice a Faransa.

Mista Cope ya kare matakinsu yana mai cewa iyayen da suka shigo Faransa ta barauniyar hanya ba su da izinin samun shedar zama ‘yan kasa.

A tsarin dokar Faransa duk ‘yayan da aka Haifa a Faransa suna da ‘Yancin samun shedar zama ‘yan kasa idan sun kai shekaru 18 kuma sun kwashe tsawon shekaru akalla 5 zuwa 11 a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.