Faransa- Sarkozy zai kalubalanci sirrin rayuwar shi da aka wallafa
Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy tare da matarsa Carla Bruni sun dauki matakin shari’a domin kalubalantar bayanan sirrin rayuwarsa da aka dauka ba tare da saninsu ba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Lauyan da ke kare Tsohon shugaban yace sun dauki matakin ne domin kada a sake wallafa bayanan sirrin da suka shafi rayuwar Sarkozy da Matarsa.
Wani tsohon na hannun damar Sarkozy ne mai suna Partick Buisson, ake zargi ya dauki zantukan rayuwar tsohon shugaban da matarsa, da wasu bayanai da suka shafi siyasa
Masu sharhi dai suna ganin wannan zai iya haifar da barakar Siyasa ga Sarkozy.
Akwai mujallar Le Canard da Atlantico a Intanet da suka wallafa labarin game da bayanan sirrin na Sarkozy.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu