Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy ya nisanta kansa da siyasar Faransa

Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy, ya ce ba ya da niyyar sake dawowa a fagen siyasar kasar, kwanaki kadan bayan da kotun Tsarin Mulkin kasar ta rufe asusun ajiyar jam’iyyarsa ta UMP.

Tsohon shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy
Tsohon shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy Reuters/Philippe Wojazer
Talla

Tsohon Shugaban wanda ya sha kaye a hannun Francois Hollande, dan takarar jam’iyya masu ra’ayin gurguzu a zaben da ya gabata, ya dan soma fito wa ne a bainar jama’a a daidai lokacin da aka rufe asusun ajiyar yakin neman zabensa na shekarar da ta gabata.

Sarkozy, ya ziyarci ofishin jam’iyyarsa ta UMP, inda ya sami gagarumin tarbe daga magoya bayansa, yayin da wasu ke cewa hakan ba ya rasa nasaba da kokarin da tsohon shugaban ke yi domin sake komawa a fagen siyasar kasar.

Sai dai a lokacin da ya ke mayar da martani a shafinsa na Twitter, Sarkozy, ya ce wannan ba ya nufin dawowarsa a fagen siyasa, kuma idan lokacin yin Magana da Faransawa ya yi, zai yi hakan.

A Makon jiya ne Kotun Tsarin Mulkin kasar ta rufe asusun tara kudaden yakin neman zaben Sarkozy, wanda ke kunshe da Euro Milyan 11 kwatankocin Dala Milyan 13, kudaden da kotun ta ce adadinsu ya yi yawa a matsayin kudaden yakin neman zabe karkashin dokokin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.