Isa ga babban shafi
Faransa

Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya gurfana gaban kotu

Lauyan Nicolas Sarkozy ya ce kotu a kasar ta tuhumi tsohon shugaban kasar ta Faransa bisa zargin sa da karbar makuddan kudade daga hannun wata shahrarriyar attajira da ke kasar mai suna Liliane Bettencourt.

Nicolas Sarkozy, tsohon shugaban Faransa
Nicolas Sarkozy, tsohon shugaban Faransa REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Lauyan na Sarkozy mai suna Thierry Herzog ya ce tuni ya shigar da kara a gaban wata kotun inda yake kalubalantar wannan zargi da ake yi wa wanda yake karewa.

A jiya alhamis ne dai kotun ta sake gayyatar tsohon shugaban kasar ta Faransa da kuma wani jami’i da ke aiki da kamfanin Bettencourt a gabanta, kuma babban dalilin da ya sa alkalin kotu ya gayyace su Nikola Sarkozy da kuma Pascal Bonnefoy mai yi wa shahararriyar attajirar ta kasar Fransa hidima Liliane Bettencourt domin bayyana a gabansa a wannan karo shi ne, sanin ko sau nawa ne tsohon shugaban kasar ya ziyarci gidan attajirar a lokacin yakin neman zabensa na shekara ta 2007.

Shaidu dai sun ce ko shakka babu Pascal Bonnefay ya shiga ginin kotun a tsakiyar ranar jiya, to sai dai ba wanda ya ga lokacin da Sarkozy ya shiga a cikin ginin kotun.

A karon farko da ya bayyana a gaban alkalin da ke binciken zargin da ake yi masa na karbar Euro milyan 5 da digo biyu daga wannan attajira a lokacin yakin neman zabensa duk da cewa dokokin Faransa sun haramata wa ‘yan takara yin hakan, a watan nuwambar shekarar da ta gabata Sarkozy ya ce shi kam sau daya ya taba zuwa gidan attajirar shi kuma domin ganawa ne da mijinta.

A wani zama da kotun ta taba yi a 2010, wata acoountan a kamfani Betencourt mai suna Claire Thibout ta ce ita da kanta ce ta dankawa ta hannun damar attajirar mai suna Patrice De Maistre da wata ambulam dauke da makuddan kudade domin bai wa ma’ajin kudi na kwamitin yakin neman Sarkozy wato Eric Woerth.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.