Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy ya nemi a sake zaben shugabannin Jam’iyyarsu

Tsohon Shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya bukaci sake gudanar da zaben shugabanin Jam’iyarsu ta UMP, sakamakon takaddamar da aka samu tsakanin ‘Yan takarar shugabancin Jam’iyyar guda biyu al'amarin da ke neman rusa jam’iyar.

Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy a harabar ofishin Jam'iyyarsu ta UMP
Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy a harabar ofishin Jam'iyyarsu ta UMP REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Gardama ta tashi ne tsakanin Tsohon Firminista, Francois Fillon da Sakataren Jama’iyar, Jean Francois Cope, lokacin da aka gudanar da zaben, inda dukkaninsu suka aiyana kansu a matsayin wadanda suka samu nasarar lashe zaben shugabancin Jam’iyyar.

Tsohon Firaminista, Alain Juppe ya yi, kokarin sasanta rikicin ‘Yan takarar biyu amma hakan ya ci tura, kodayake kwamitin zaben ya bayyana Cope a matsayin zababben shugaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.