Isa ga babban shafi
Faransa

Jam’iyyar UMP ta Sarkozy ta kama hanyar Rugujewa

Jam’iyar UMP ta tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy ta kama hanyar rugujewa, sakamakon kasa sasanta bangarori biyu, da ke rikicin neman shugabancin Jam’iyyar bayan gudanar da zaben.

Alain Juppé da François Fillon da  Jean-François Copé
Alain Juppé da François Fillon da Jean-François Copé REUTERS/Charles Platiau/Files
Talla

Alain Juppe, yace kokarin sasanta bangarorin biyu ya ci tura bayan kwashe lokaci yana tattaunawa da Tshon Firaminista Francois Fillon da Jean-Francois Cope da aka ce ya lashe zaben.

Yanzu haka kuma Francois Fillon yace zai shigar da kara a Kotu bayan zargin magudi a zaben shugabancin Jam’iyyar.

Alain Juppé, ya yi fatan ganin ya zama mai samar da masalaha domin mayar da zaman lafiya a babbar jam’iyar ‘yan adawa, da ta samu kanta cikin halin ja in ja tsakanin tsohon Firaministan Gwamnatin Nicolas Sarkozy, François Fillon, da Jean-François Copé.

Fillon mai shekaru 58 da Cope mai shekaru 48 sun soki juna tare da zargin tabka magudi a zaben da aka gudanar a karshen makon jiya.

Mista Cope ne dai aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben bayan samun rinjayen kuri’u.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.