Isa ga babban shafi
Faransa

Wasu Alkalan Faransa sun bukaci Sarkozy ya gurfana a gaban kotu akan batun Karachi

Rahotanni daga Faransa sun ce Alkalan kasar sun nemi a gurfanar da Sarkozy game da wata sanarwa da ta fito daga Fadar Elysee a zamanin shi akan harin da aka kai a Karachi wanda ya kashe Faransawa 11.

Tsohon shugaban kasar Faransa  Nicolas Sarkozy
Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Sanarwar da aka fitar daga Fadar Sarkozy a lokacin ta wanke Sarkozy daga batun na Karachi bayan kai hari a 2001 da ya kashe masana Fasahar Faransa a Pakistan.

Tuni dai Iyalan Injiniyoyin suka shigar da kara don kalubalantar Sanarwar suna masu cewa ta saba dokar da haramta wallafa wani bayani a wata shari’a da ake ci gaba da gudanarwa.

A Zamanin Sarkozy Masu gabatar da kara sun ce Tsohon Shugaban yana da kariyar da ba zai gurfana ba a gaban kotu.

Wata Majiya dai tana zargin an kai wa Faransawa Hari ne a lokacin don mayar da martani ga Faransa saboda kin bayar da cin hanci ga jami’an Pakistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.