Isa ga babban shafi
Faransa

Gwamnatin Hollande ta cika kwanaki 100 a Faransa

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande a yau talata ne gwamantin shi ke bukin cika kwanaki 100 da kama aiki bayan zaben shi shugaban kasa. Masu lura da lamura na ganin shugaban yana da jan aiki na ganin ya samar da aikin yi ga Faransawa masu zaman kashe wando, tare da farfado da tattalin arzikin kasar da ya samu nakasu.

Shugaban kasar Faransa  François Hollande.
Shugaban kasar Faransa François Hollande. REUTERS/Robert Pratta
Talla

Bukin na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban ke hutu, kodayake ya katse hutunsa domin ziyartar ‘Yan sandan da aka bindige a watan Yuni.

Shugaban ya fara fuskantar Suka daga bangaren Jam’iyyar Adawa ta UMP akan matsayinsa game da rikicin Syria ta la’akari da yadda Sarkozy ya jagoranci kasashen Turai a rikicin Libya a bara.

Bayan cika kwanaki 100, Jaridun Faransa sun ce shugaban har yanzu bai san madafar shi ba.

Jaridar Liberation tace Faransawa sun fara shakkun gwamnatin Hollande wajen magance matsalolin da Faransa ke fuskanta.

A cewar Jaridar Liberation har yanzu Faransawa sun kasa fahimtar alkiblar gwamnatin Hollande.

A wani bincike na jin ra’ayin Jama’a da aka gudanar, sakamakon ya nuna kashi 54 na Faransawa sun bayyana damuwarsu game da ayyukan Hollande zuwa yanzu kuma kashi 51 sun ce abubuwa sun tabarbare tun da aka rantsar da shi zuwa yanzu.

A Wani jerin ajin matsayi da mujallar Journal du Dimanche ta fitar a makon jiya, Hollande shi ne a matsayi na 15 cikin jerin sunayen manyan mutane a Faransa inda shugaban ya ke kusa da matsayin  dan wasan Tennis Yannick Noah da dan wasan kwallon kafa Zinedine Zidane.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.