Isa ga babban shafi
Faransa

Tattalin Arzikin Jamus da Faransa na tafiyar hawainiya

Rahotan watanni uku-uku game da matsayin tattalin arzikin kasashen Turai masu amfani da takardar kudin Euro, na nuni da cewa tattalin arzikin Faransa da na Jamus, ya tsaya cik ba tare da an samu wani ci gaba ba a cikin watannin ukun da suka gabata.

François Fillon, Alain Juppé, Jean-Pierre Raffarin Jiga jigan Jam'iyyar UMP mai adawa a Faransa
François Fillon, Alain Juppé, Jean-Pierre Raffarin Jiga jigan Jam'iyyar UMP mai adawa a Faransa REUTERS/Charles Platiau
Talla

Tuni dai babbar jam’iyyar adawa a kasar Faransa UMP ta bakin Eric Worth tsohon minista a gwamnatin Nicolas Sarkozy ta yi kakkausar suka ga gwamnatin shugaba Francois Hollande dangane da wannan koma-baya.

A cewarsa wannan abin dariya ne, domin suna kokarin nunawa duniya cewa siyasar tsuke bakin aljihu da gwamnatinsu ke aiwatarwa siyasa ce mai kyau, alhali kuwa ba haka ba ne.

Worth yace abin da ke faruwa shi ne, gwamnatin Hollande ta kasa cike gibin tattalin arziki da kasar ke fama da shi sannan kuma tana kashe kudaden jama’a a hanyoyin da ba su da amfani tare da kara nauyin haraji akan jama’a.

Jamn’iyyar UMP ta suka sha kaye a zaben 2011 tace wadannan su ne dalilan da suka sa Faransa ta tsinci kanta a cikin mawuyacin hali musamman a bangaren ci gaban tattalin arziki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.