Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa da Jamus sun tuna Sojojin da suka Mutu a Yakin duniya

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande da takwaransa na Jamus Joachim Gauck sun girmama miliyoyin Sojojin da suka mutu a yakin duniya na farko, a dadai lokacin da ake cika shekaru 100 da kasar Jamus ta kaddamar da yaki a kan Faransa.

Shugaban Faransa Francois Hollande da Joachim Gauck na Jamus a yankin Hartmannswillerkopf  gabacin Faransa suna girmama Sojojin da suka mutu a yakin Duniya
Shugaban Faransa Francois Hollande da Joachim Gauck na Jamus a yankin Hartmannswillerkopf gabacin Faransa suna girmama Sojojin da suka mutu a yakin Duniya Reuters/Thibault Camus
Talla

Shugabannin biyu sun hadu ne a wani tsauni a lardin Alsace da ke kusa da kan iyaka da kashen biyu inda aka kashe Sojoji sama da 30,000.

A jawabin shugabannin sun danganta al’amarin da ya faru a tsakaninsu da suka dade suna gaba a shekarun baya a matsayin wani darasi ga duniya musamman rikicin Isra’ila da Hamas da ya lakume rayukan mutane kusan 2000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.