Isa ga babban shafi
Faransa

An nadi bayanan Sarkozy na Tarho

Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy da ke fuskantar badakalar rashawa, an sake bankado wasu bayanansa da aka nada a wayar tarho yana tattauna yadda zai taimakawa wani alkali a Monaco.

Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy
Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy Screen capture/TF1
Talla

Sarkozy da ake tuhuma akan badakalar rashawa a yakin neman zabensa a 2007 yace ana yi masa zagon kasa ne a siyasance.

A yau Assabar Jaridar Le Monde ta wallafa kalaman Sarkozy da aka nada a wayar shi ta salula, inda tsohon Shugaban ke neman alfarmar samar wa wani alkali aiki a Monaco domin saka ma sa da alherin taimakon da ya yi masa akan daya daga cikin tuhume tuhumen da ake wa masa.

An bayyana cewa an nadi bayanan ne na Sarkozy a cikin watan Fabrairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.