Isa ga babban shafi
Faransa

Nicolas Sarkozy ya gurfana gaban 'yan sandan Faransa

Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, a safiyar yau talata ya bayyana a gaban jami’an hukumar ‘yan sandan kasar domin amsa tambayoyi dangane da zargin karbar rashawa da ake yi masa.

Nicolas Sarkozy na waya
Nicolas Sarkozy na waya REUTERS/Yves Herman
Talla

A karkashin dokokin kasar dai, ‘yan sanda na da damar tsare tsohon shugaban har na tsawon sa’o’i 24 sannan kuma suna da hurumin kara wasu sa’o’in 24 domin ci gaba da yi masa tambayoyi. Ana dai zargin Sarkozy ne da kokarin tauye binciken da ake yi masa game da karbar rashawa a lokacin yakin neman zaben shekara ta 2007.

A ranar litinin da ta gabata ne aka cafke lauyan tsohon shugaban mai suna Thierry Herzog da kuma wasu alkalai biyu da ake zargin cewa suna yi wa aikin binciken zagon kasa.

Wannan lamari dai na ci gaba da haifar da shakku a game da makomar Sarkozy a fagen siyasar kasar Faransa, musamman ma batun tsayawarsa takarar neman shugabancin kasa a shekara ta 2014 idan Allah ya kai mu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.