Isa ga babban shafi
Faransa

Shugaba Sarkozy ya zargi 'yan adawa kan muzanwa

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya tsallake rijiya da baya yammacin jiya Alhamis, yayinda wasu ‘yan jamiyyar adawa suka hango shi, a ci gaba da yawon neman kuri'un jama'a a zaben Shugaban kasar dake tafe watan gobe na Afrilu.

Reuters / Philippe Wojazer
Talla

Sakamakon wurginsa da danyen kwai da bakaken kalamai da wasu suka yi ta yi masa gaba-da-gaba, saida takai ‘yan sandan da jami'an tsaro sun kwashe shi zuwa wata mashaya suka boye shi, saida kura ta lafa.

Daga bisani saida ‘yan sanda suka killace harabar mashayan mai suna Bar Du Palais dake Bayonne, kafin a fitar da Shugaban kasar ya yi gaba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.