Isa ga babban shafi
Faransa-China

China da Faransa sun karfafa kawancen kasuwanci

Kasashen China da Faransa, sun kulla yarjejeniyar kasuwanci na kudi dala biliyan 18, a lokacin da shugaba Xi Jingping ya kai wa takwaransa na Faransa Francois Hollande ziyara.

Shugaban China  Xi Jinping tare da Shugaban Faransa François Hollande a birnin Paris
Shugaban China Xi Jinping tare da Shugaban Faransa François Hollande a birnin Paris REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Shugabannin biyu sun sanya hannu ne yarjeniyoyi a fannin da ya shafi samar da ayyukan yi da suka shafi fannoni daban daban har guda hamsin.

Babbar yarjejeniyar ita ce sayen jiragen sama samfarin Airbus guda 70 da China za ta yi a hanun Faransa, wadanda aka kiyasta za a saye kan kudi dala Biliyan Goma.

Baya ga bangaren sufurin jiragen sama, kasashen biyu sun sake kulla yarjejeniyar a fannin makamashin nukiliya da kuma hada hadar kudade.

Huldar kasuwanci dai tsakanin China da Jamus ta fi karfi fiye da kawancen Jamus da Faransa

Sai dai baya ga harkokin kasuwanci da shugabannin biyu suka fi mayar da hankulansu a kai, sun kuma tattauna game da batun rikicin kasar Ukraine, inda Shugaba Hollande ya nuna gamsuwarsa da yadda China ta soki Rasha game da Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.