Isa ga babban shafi
Faransa

Jinping na ziyarar kwanaki uku a kasar Faransa

Ziyarar ta kwanaki uku da shugaban China Xi Jinping ya kawo a Faransa na zuwa ne a daidai lokacin da huldar diflomasiyar kasashen biyu ke cika shekaru 50.

Xi Jinping, shugaban China
Xi Jinping, shugaban China REUTERS/John Thys
Talla

Kodayake Karfin huldar kasuwanci da ke tsakanin Faransa da China ba ta kai karfin dangantakar ciniki da ke tsakanin Jamus da China ba, amma wannan ziyarar akwai jerin yarjejeniyoyi da shugabanin biyu za su kulla ta fannin kasuwanci
Wadanda suka kunshi yarjejenyar Nukiliya da Noma da ta jiragen sama.

Kodayake babu wasu bayanai da aka fitar akan kawancen kasuwancin da kasashen biyu za su kulla, amma akwai yarjejeniyar da aka tabbatar tsakanin Kamfanin Dongfeng na kera motoci a China da kuma kamfanin Peugeot na Faransa.

Akwai kuma yarjejeniya akan kera jiragen sama masu saukar angulu na fararen hula tsakanin China da Faransa.

Inda tun a ziyarar Hollande a China a watan Afrliun bara, shugaba Xi ya yi alkawalin sayen jiragen Faransa na Airbus. Haka kuma kamfanin areva na Faransa yana fatar a cimma yarjejeniya da China kan batun nukiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.