Isa ga babban shafi
Faransa

Shugaban China Jinping na ziyarar aiki a Faransa

Shugaban kasar China Xi Jinping wanda ke tare da gagarumar tawaga cikinsu kuwa har da mai dakinsa Peng Liyuan, na gudanar da ziyarar aiki ta tsawon kwanaki a Faransa daga yau talata.

xi jinping shugaban China
xi jinping shugaban China
Talla

A lokacin wannan ziyara, Jinping zai halarci bukukuwa na musamman da ake shirya kan cikar kasashen biyu shekaru 50 da kulla alakar diflomasiyya a tsakaninsu, yayin da batun kulla kasuwanci a tsakanin kasashen biyu zai kasance jigo a lokacin da shugaban na China zai gana da mai masaukinsa Francois Hollande.

Ana kyautata zaton cewa ko baya ga yarjeniyoyi da mutanen biyu za su sanya wa hannu, shugaban Hollande zai kuma shiryawa Jinping lifayar girmamawa a fadar shugaban kasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.