Isa ga babban shafi
Faransa

Jam’iyya mai mulki a Faransa ta fidda sabbin Dabaru

Jam’iyyar gurguzu mai mulki a Faransa ta fitar da wasu sabbin tsare tsare domin samun farin jinin Faransawa yayin da Jam’iyyar ke fuskantar baraka daga Jam’iyyar ‘Yan kishin kasa ta National Front a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a karshen mako

Jagoran Socialists a Faransa Hollande
Jagoran Socialists a Faransa Hollande blog.heritage.org
Talla

Jam’iyyar ta Front Nationale dai yanzu haka ta kama hanyar lashe kujerun kanan hukumomi 15 a sassan yankunan Faransa, a zagaye na farko da aka gudanar a zaben.

A sakamakon zaben zagaye na farko ana ganin zai tursasa wa shugaba Hollande na Jam’iyyar gurguzu da ke fuskantar adawa yin garanbawul a gwamnatinsa, yayin da Jam’iyyar ‘yan kishin kasa ta Marine Le Pen's da ke adawa da bakin haure ke masa barazana.

Akwai ‘yan takara daga Jam’iyyar Marine Le pen da za’a fafata da su a zagaye na biyu a zaben, inda tuni suka lashe kujerar magajin gari guda na Henin Beaumont (inabumu) da gagarumin rinjaye.

Yanzu haka Jam’iyyar gurguzu ta fitar da sanarwar kulla kawance da wasu jam’iyyun adawa domin dakile barazanar ‘Yan kishin kasa.

Ana sa ran Hollande zai yi wa gwamnatinsa garanbawul ne, bayan kammala zaben inda ake sa ran Ministan cikin Gida Manuel Valls zai karbi mukamin Firaiminista.

Ana dai kallon zaben a matsayin wani Zakaran gwajin dafi don auna farin Jinin gwamnatin gurguzu a Faransa.

Inda shugaban Hollande ke fuskantar suka daga jama’ar kasar da dama, sakamakon yadda ya ke tafiyar da siyasarsa ta cikin gida da kuma batutuwan da suka shafi tattalin arzikin kasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.