Isa ga babban shafi
Italiya

An ceto bakin haure 2,000 a Italiya

Mahukuntan kasar Italiya sun ce sun kubutar da bakin haure sama da 2,000, yawancinsu daga kasashen arewacin Afrika a tsibirin Sicily da ke gabar teku. Wannan kuma na zuwa ne bayan mahukuntan Spain sun ce akwai mutane 500 da suka nemi shiga cikin kasar.

Wasu bakin haure dake kokarin ketarawa zuwa nahiyar Turai daga Afrika
Wasu bakin haure dake kokarin ketarawa zuwa nahiyar Turai daga Afrika REUTERS
Talla

Dubban bakin haure ne ke tsallakwa zuwa kasashen Turai ta hanyar shiga Spain da Italiya, yawancinsu daga kasashen Afrika.

Wannan ne ya sa kasashen Spain da Italiya suka tsaurara matakan tsaro tare da neman taimakon Kungiyar Tarayyar Turai.

A bara kawai hukumar kula da kan iyakokin Turai tace sama da mutane 20,000 ne suka nemi shiga cikin kasar Italiya. A irin haka ne wasu suka nutse a cikin teku kusa da tsibirin Lampedusa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.