Isa ga babban shafi
Rasha-Saudiya

Rasha ta karyata cinikin makamai tsakaninta da Saudiya

Gwamnatin kasar Rasha ta karyata rahoton da ke cewa shugaba Putin ya gana da babban jami’in leken Asirin Saudiya game da cinikin makamai domin samun sauyin kasuwa daga Syria. A ranar 31 ga watan Yuli ne Shugaba Putin ya yi wata ganawar sirri da Yarima Bandar bin Sultan a birnin Moscow.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin
Talla

Wata majiyar Diflomasiya tace Saudiya ta nemi Rasha ta katse huldar da ke tsakaninta da bashar Assad na Syria amma Shugaba Putin ya yi watsi da bukatar, inda Saudiya tace idan ya amince zasu kulla cinikin makamai.

Gwamnatin Rasha ta dade tana bayyana goyon bayanta ga gwamnatin Assad na Syria yayinda kuma Saudiya ke adawa da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.