Isa ga babban shafi
Rasha

Kotu ta daure shugaban masu adawa da Putin a Rasha

Kotun kasar Rasha ta yanke hukuncin daurin shekaru biyar ga shugaban masu zanga-zangar adawa da shugaba Vladimir Putin bayan kama shi da lafin cin hanci da yin sama da fadi da kudaden wani kamfanin Katako.

Alexeï Navalny babban mai adawa da gwamnatin Putin
Alexeï Navalny babban mai adawa da gwamnatin Putin REUTERS/Sergei Karpukhin
Talla

Alexei Navalny ya yi watsi da hukuncin na Kotun yana mai danganta hukuncin da Siyasa.

Tuni kuma Amurka da kungiyar kasashen Turai suka yi Allah waddai da hukuncin, a wani mataki da ake ganin zai iya gurgunta huldar diflomasiya tsakanin Rasha da kasashen.

Navalny mai shekaru 37, shi ne babban mai adawa da Jam’iyya mai mulki ta Vladimir Putin. Bayan yanke masa hukuncin dan adawar ya bukaci magoya bayan shi su ci gaba da adawa da gwamnati.

A can lokuttan baya, Navalny yace yana fatar tsaya wa takarar shugaban kasa inda tuni ya yanki rijistar tsayawa takarar magajin gari a Moscow, amma saboda wannan hukuncin dole ya fice daga takara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.