Amurka tana fushi da Rasha game da Snowden
Amurka ta bayyana damuwa tare da gargadin Rasha game da mafaka da taba jami’in leken asiri Edward Snowden da Amurka ke nema ruwa a jallo bayan ya fallasa sirinta. Snowden ya samu zantawa da ‘Yan rajin kare hakkin bil’adama wadanda ya shaidawa yana bukatar mafaka a Rasha.
Wallafawa ranar:
Snowden ya kwashe tsawon makwanni uku a makale a cikin kasar Rasha, kuma a karon farko a ranar Juma’a jami’in leken asirin ya fito a bainar jama’a domin ganawa da ‘Yan rajin kare hakkin dan Adam.
Gwamnatin Amurka tana bukatar a mika mata Snowden domin fuskantar Shari’a akan bayanan sirrin Amurka na zantukan mutane ta wayar salula da Snowden ya fallasa. Kasar Rasha kuma ta yi watsi da wannan bukatar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu