Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Snowden ya ce baya cikin fargaba

Tsohon jami’in leken asirin kasar Amurka Edward Snowden, da ake nema ruwa a jallo yace baya cikin wata fargaba ko yin nadama ga ayyukansa na kwarmata bayanan sirrin Amurka. 

Edward Snowden, da Amurka ke nema ruwa a jallo
Edward Snowden, da Amurka ke nema ruwa a jallo REUTERS/Glenn Greenwald
Talla

Dan jaridar Guardian da ya fara yada bayanan sirrin Amurka da suka fito daga Snowden, Glenn Greenwald yace dan tonon asirin yana cike da farin ciki akan yadda labarinsa ya canjo sa’insa tsakannin kasashen Duniya

A wata hira da kamfanin dillacin labaran faransa na AFP, Dan jaridar yace akwai yiyuwar Snowden zai yi rayuwa a Venezuela, kasar da ta amince ta ba shi mafaka.

Dan jaridar yace ya kwashe tsawon makwanni biyu ba tare da zantawa da Snowden ba, tun lokacin da ya fice Hong Kong amma ya samu ganawa da shi a ranar Talata da ta gabata.

Dan jaridar wanda yanzu haka ke zama a birnin Rio de Janeiro yace Snowden baya cikin fargaba ko nadama ga ayyukkan kwarmata bayan sirrin Amurka.

Snowden da ya makale a Birnin Moscow na kasar Rasha, kuma ya nemi mafaka a kasashe sama da 20 domin gujewa hukunci daga hukumomin birnin Washington.
Kuma zancen Snowden shi ne ya kara fito da barakar da ke tsakanin kasashen yankin Latin da Amurka musamman Venezuela da Bolivia da suka ce zasu bai wa dan kwarmaton mafaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.