Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka

Inganta Huldar Rasha da Amurka ta fi Snowden, inji Putin

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yace inganta huldar da ke tsakanin Amurka da Rasha ta fi karfin batun Snowden Amurka ke nema ruwa a jallo bayan ya kwarmata tono asirinta, kuma wanda ya mika takardarsa ta neman mafaka a Rasha.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Kamfanin Dillacin labaran Rasha na RIA Novosti ya ruwaito kalaman Putin yana cewa inganta kawancen kasahen biyu ya fi muhimmanci fiye da batun Snowden.

Kalaman na shugaba Putin na zuwa ne bayan Amurka ta bukaci Rasha ta yi watsi da bukatar Snowden wanda ta ke neman a mika mata shi.

Snowden dai ya makale ne a Rasha bayan ya fito daga Hong Kong tun a ranar 23 ga watan Yuni.

Amma tun a farko, Putin ya bukaci dan tonon asirin ya gaggauta ficewa daga Rasha don kada ya fada tarkon Amurka, wanda shi ne karon farko da shugaba Putin ya yi furuci game da dan tonon asirin.

Mista Putin yace Snowden ya shigo Rasha ne ba tare da yawun bakinsu ba illa ya makale ne bayan ya fito daga Hong Kong.

Shugaban na Rasha yace Snowden zai gaggauta ficewa daga Rasha zuwa kasashen da suka amince su ba shi mafaka don gudun kada ya fada tarkon Amurka.

Putin wanda ya gabatar da jawabi a Kafar Talabijin ya zargi Amurka wajen bin hanyoyin haramtawa dan tonon asirin ficewa daga Rasha, domin Amurka ta tsorata sauran kasashe da ke da niyyar ba Snowden mafaka, lamarin da Putin yace Amurka ta kullawa Snowden tarko a Rasha.

Amma a baya shugaba Putin yace Rasha tana iya ba Snowden mafaka idan har ya jingine tono bayanan sirrin Amurka.

Batun Snowden dai kan iya kara gunguncewar dangantaka tsakanin Amurka da Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.