Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Obama ya soke kudirin ganawar shi da Putin saboda Snowden

Shugaban Amurka Barack Obama ya rusa kudirin ganawar shi da shugaban Rasha Vladimir Putin a watan gobe kamar yadda sanarwar ta fito daga Fadar White House. Wannan kuma wata manuniya ce ga fushin Amurka akan mafakar da Snowden ya samu a Rasha.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Larry Downing
Talla

Tun da farko gwamnatin Obama ta bayyana bacin ranta game da mafakar da Rasha ta ba Snowden wanda ta nema a mika mata shi bayan ya fallasa sirrin kasar.

A cikin sanarwar, Amurka tace akwai gazawa daga Rasha ga ci gaban huldar kasashen biyu musamman yarjejeniyar takaita cinikin makamai da huldar kasuwanci da batun sha’anin tsaro da hanyoyin kare hakkin bil’adama.

Shugaba Obama yace zai kai ziyara kasar Sweden a lokacin da zai halarci taron kasashen G8 masu karfin tattalin arzikin duniya da za’a gudanar a St. Petersburg kasar Rasha a watan Satumba.

Snowden ya kwashe kwanaki a tashar jirgin Moscow bayan ya fito daga Hong Kong, kuma daga karshe jami’in leken asirin na Amurka ya samu makafa ta wuccin gadi a Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.